النازعات
ابوبكر محمود كومي · (Hausa] هَوُسَ
١.
Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi
٢.
Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi
٣.
Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo
٤.
Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre
٥.
Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni
٦.
Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa
٧.
Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye
٨.
Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne
٩.
Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu
١٠.
Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu
١١.
Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu
١٢.
Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya
١٣.
To, ita kam, tsãwa guda kawai ce
١٤.
Sai kawai gã su a bãyan ƙasa
١٥.
Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka
١٦.
A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã
١٧.
Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi
١٨.
Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka
١٩.
Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa
٢٠.
Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma
٢١.
Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni)
٢٢.
Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri
٢٣.
Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira
٢٤.
Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka
٢٥.
Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko
٢٦.
Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah
٢٧.
Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta
٢٨.
Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta
٢٩.
Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta
٣٠.
Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta
٣١.
Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta
٣٢.
Da duwatsu, Yã kafe ta
٣٣.
Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku
٣٤.
To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo
٣٥.
Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata
٣٦.
Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani
٣٧.
To, amma wanda ya yi girman kai
٣٨.
Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya)
٣٩.
To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma
٤٠.
Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai
٤١.
To, lalle ne Aljanna ita ce makõma
٤٢.
Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta
٤٣.
Me ya haɗã ka da ambatonta
٤٤.
Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake
٤٥.
Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta
٤٦.
Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa