٦.Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne
١٤.Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyawun mãsu halittawa
١٧.Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba
١٨.Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne
١٩.Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci
٢٠.Da wata itãciya,* tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ
٢١.Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni* mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ
٢٣.Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba
٢٤.Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko
٢٥.Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci
٢٧.Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idon Mu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne
٢٨.Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai
٢٩.Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa
٣٢.Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba
٣٣.Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã
٣٤.Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne
٣٥.Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da kasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne
٣٧.Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa,* kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba
٣٨.Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba
٤١.Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai
٤٤.Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni
٤٧.Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne
٥٠.Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã* Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari
٥١.Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi* kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne
٥٢.Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa
٥٣.Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu,* kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su
٦٠.Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu
٦١.Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri)
٦٢.Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su
٦٣.Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne
٦٦.Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya
٦٨.Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu
٧٠.Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne
٧١.Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton* (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa
٧٢.Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa
٧٥.Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa
٧٦.Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba* sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u
٨٠.Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba
٨٢.Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lale ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne
٨٣.Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko
٨٨.Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani
٩١.Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa
١٠٠.Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su
١٠١.Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba
١٠٣.Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama
١٠٧.Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci
١٠٩.Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi
١١٠.Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõ Na kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya
١١١.Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo
١١٥.Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba
١١٦.Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja
١١٧.Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara