٦.Abin da yake a cikin sammai nãsa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya
١٠.A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar
١٢.Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka* Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa
١٤.Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni
١٥.Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa
١٦.Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka
١٨.Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci* na dabam a gare ta
٣٩.Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan gan iNa
٤٠.A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi* kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã
٤٧.Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya
٤٨.Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwa azãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya
٥٣.Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi* Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam
٥٥.Daga gare ta* Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam
٥٨.To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa
٦١.Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe
٦٣.Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku* game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya
٦٤.Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta
٦٦.Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri
٦٩.Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je
٧١.Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba)
٧٢.Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne
٧٣.Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kuma Mafi wanzuwa
٧٤.Lalle* shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa
٧٥.Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka
٧٦.Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku
٧٧.Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riska, kuma bã ka fargabar nutsẽwa
٨٠.Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku
٨١.Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har fushĩ Na ya sauka a kanku. Kuma wanda fushĩ Na ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi
٨٢.Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa
٨٦.Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna
٨٧.Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka* ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa
٨٨.Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta
٨٩.Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni
٩٠.Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umarnĩna
٩٤.(Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba
٩٦.(Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini
٩٧.(Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi,* sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa
٩٨.Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci* dukkan kõme da ilmi
٩٩.Kamar wancan ne Muke lãbartãwa* a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gun Mu
١٠٢.A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu
١٠٣.Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma
١٠٤.Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda
١٠٨.A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya
١٠٩.A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da ya yi magana
١١١.Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe
١١٢.Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa
١١٣.Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa
١١٤.Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa* da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi
١١٥.Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shi ba
١١٦.Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya
١١٧.Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi* ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala
١٢٠.Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa
١٢١.Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace
١٢٣.Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala
١٢٤.Kuma wanda ya bijire* daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho
١٢٦.Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyin Mu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka
١٢٧.Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita,* kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa
١٢٨.Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula
١٢٩.Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta
١٣٠.Sai ka yi haƙuri* a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda
١٣١.Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikin sa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa
١٣٢.Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani Arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa
١٣٣.Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba
١٣٤.Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu
١٣٥.Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa