ابوبكر محمود كومي · (Hausa] هَوُسَ

١.(Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ãyõyi bayyanannu a cikinta, dõmin ku riƙa tunãwa
٣١.Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan* ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo
٣٣.Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu,* dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai
٥٨.Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni* sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyin Sa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima
٦١.Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku,* gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali