٢.Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa
٣.Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta
٥.Ã'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko
٧.Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato* idan kun kasance ba ku sani ba
٩.Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa
١٠.Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku,* a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta
١١.Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta
١٣.Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku
١٧.Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun* riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa
١٨.Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa
١٩.Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurin Sa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdar Sa. kuma bã su gajiya
٢٢.Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa
٢٤.Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne
٢٥.Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini
٢٨.Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõron Sa
٢٩.Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai
٣٠.Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke,* sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba
٣١.Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa
٣٥.Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku
٣٦.Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta ne
٣٩.Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba
٤٠.Ã'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba
٤١.Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su
٤٢.Ka ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu
٤٣.Ko kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su* ba daga gare Mu
٤٤.Ã'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage* ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya
٤٥.Ka ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi
٤٦.Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci
٤٧.Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi
٤٨.Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa
٥٦.Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka
٥٧.Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya
٦٣.Ya ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana
٦٥.Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana
٦٦.Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah
٧٣.Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurnin Mu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu
٧٤.Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai
٧٦.Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma
٧٧.Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya
٧٨.Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu
٧٩.Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar)* ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa
٨٠.Kuma Muka sanar da shi sana'ar* wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne
٨١.Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme
٨٢.Kuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su
٨٣.Kuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama
٨٤.Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurin Mu da tunãtarwa* ga mãsu ibãda
٨٧.Kuma mai kifi* a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai
٨٨.Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni
٨٩.Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo
٩٠.Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata* masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu
٩١.Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.* Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya
٩٢.Lalle ne wannan* ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini
٩٤.Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne
٩٧.Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci
٩٨.(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin* da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne
٩٩.Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne
١٠١.Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne
١٠٢.Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa
١٠٣.Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi
١٠٤.A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon* halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa
١٠٥.Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato* (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩna sãlihai, sunã gãdonta
١٠٦.Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta* ga waɗansu mutãne mãsu ibãda)
١٠٨.Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne
١٠٩.Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci
١١١.Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci
١١٢.Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa