٤.Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji
٥.Kuma lalle nĩ, na ji tsõron* dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa
٧.(Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni
٨.Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa
٩.Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba
١٠.Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai
١١.Sai ya fita ga mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma
١٣.Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gun Mu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa
١٥.Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai
١٦.Kuma ka ambaci Maryamu* a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas
١٧.Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci
٢٠.Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba
٢١.Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi* ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce
٢٣.Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta
٢٤.Sai (yãron da ta haifa) ya* kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki
٢٥.Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu
٢٦.Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki*. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba
٢٧.Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma
٢٩.Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri
٣١.Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai
٣٣.Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai
٣٥.Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã*. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa
٣٦.Kuma lalle Allah ne Ubangijina* kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici
٣٧.Sai ƙungiyõyin* suka sãɓã wa jũna a tsakãnins u. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma
٣٨.Mẽne ne ya yi jinsu*, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna
٣٩.Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni
٤٢.A lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka
٤٣.Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici
٤٥.Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan
٤٦.Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci
٤٧.Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka.* Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni
٤٨.Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina
٤٩.To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi
٥١.Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi
٥٤.Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi
٥٥.Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens *da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa
٥٨.Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka
٥٩.Sai waɗansu 'yan bãya* suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri
٦٠.Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme
٦١.Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa
٦٢.Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice
٦٤.(Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka* Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma** (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba)
٦٥.Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãnin su. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautar sa. Shin kã san wani takwara a gare shi
٦٧.Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba
٦٨.To, Munã rantsuwa da Ubangijin ka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne
٦٩.Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya
٧٢.Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne
٧٣.Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa
٧٤.Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã
٧٥.Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna
٧٦.Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma
٩٧.Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma
٩٨.Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu